logo

HAUSA

Mahukuntan janhuriyar dimokaradiyyar Congo sun dora alhakin kisan jakadan Italiya kan ’yan tawayen FDLR

2021-02-23 14:04:59 CRI

Mahukuntan janhuriyar dimokaradiyyar Congo sun dora alhakin kisan jakadan Italiya kan ’yan tawayen FDLR_fororder_210223-saminu 4-hoto

Mahukuntan jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, sun dora alhakin kisan jakadan kasar Italiya a kasar kan ’yan tawayen FDLR.

Wata sanarwa da ma’aikatar cikin gidan kasar ta fitar, ta ce ’yan tawayen masu sansani a lardin arewacin Kivu ne suka yiwa tawagar jakada Attanasio kwantan bauna, lamarin da ya haddasa harbe jakadan, da dogarinsa, da kuma direbansa, baya ga karin wasu mutanen da dama da suka jikkata.

Jakadan da ’yan tawagarsa, na kan hanyarsu ce ta zuwa wani aikin jin kai, cikin jerin gwanon tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar, lokacin da aka bude wa tawagar wuta a yankin Rutshuru, mai nisan ’yan kilomitoci kadan daga Goma, fadar mulkin lardin arewacin Kivu.  (Saminu)