logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Sin ya bukaci Amurka ta sake nazartar manufarta kan kasar Sin

2021-02-22 10:36:18 CRI

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya yi kira ga masu tsara manufofin Amurka, su yi watsi da bangaranci da zarge-zarge marasa tushe, su sake nazartar manufofin kasarsu kan kasar Sin, domin tabbatar da kyautatuwar dangantaka tsakanin kasashen.

Wang Yi, ya bayyana haka ne a yau Litinin, lokacin da yake gabatar da jawabi a bikin bude Dandalin Tatatuanawa da Musaya na Lanting a nan Beijing. Taken dandalin shi ne “Inganta Tattaunawa da Hadin Gwiwa da Kawar da Sabani: Dawo da Dangantakar Sin da Amurka Bisa Turbar da ta Dace”

A cewar ministan, suna fatan Amurka za ta daidaita manufofinta nan bada jimawa ba, musammam cire harajin ba gaira ba dalili da ta sanyawa kayayyakin Sin da dage takunkuman da ta sanyawa kamfanonin kasar da cibiyoyin bincike da na ilimi, da watsi da matsin lambar da take yi wa ci gaban fasahohin kasar, ta yadda za a samar da sharuddan da suka dace na hadin gwiwar kasashen biyu. (Fa’iza Mustapha)