logo

HAUSA

Yawan masu COVID-19 a Ghana ya zarce 80,000

2021-02-22 11:25:59 CRI

Yayin da a ranar Lahadi aka samu sabbin masu kamuwa da cutar COVID-19 kimanin 598, jimillar mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar Ghana ya kai 80,253, hukumar lafiyar Ghana (GHS) ta sanar da hakan.

A cewar hukumar lafiyar, an samu yawan mutanen da cutar COVID-19 ta kashe a Ghana 577, sannan yawan mutanen da suke jinyar cutar a halin yanzu a kasar ya kai 6,658.

Yayin da ake cigaba da samun karuwar masu kamuwa da cutar ta COVID-19, gwamnatin Ghana da bullo da wasu jerin matakai, da suka hada da haramta taruwar jama’a da sauya tsarin ayyuka a kasar.

Hukumar GHS ta bukaci jama’a da su martaba dukkan dokokin kariya daga kamuwa da cutar, kamar sanya takunkumin rufe baki da hanci a wuraren taruwar jama’a da kuma yawaita wanke hannu.

Gwamnatin kasar Ghana ta yi alkawarin fara gagarumin shirin sanya alluran riga-kafin cutar daga makon farko na watan Maris.(Ahmad)