logo

HAUSA

IAEA ta cimma kwarya kwaryar yarjejeniya da Iran

2021-02-22 10:38:08 CRI

Hukumar kula da makamashin Nukiliya ta duniya IAEA, ta cimma kwarya kwaryar yarjejeniyar fahimtar juna da kasar Iran, a wani mataki da ceto yarjejeniyar nukiliyar kasar da aka cimma a shekarar 2015.

Da yake tsokaci game da hakan, bayan wata ziyara da ya kai kasar ta Iran, babban daraktan IAEA Rafael Grossi, ya shaidawa manema labarai cewa, Tehran ta sha alwashin dakatar da aiwatar da matakan da ta amincewa, cikin waccan yarjejeniya ta JCPOA, tun daga gobe Talata, bayan da majalissar dokokin kasar ta amince da hakan.

To sai dai kuma a hannu guda, bisa matsayar da aka cimma, IAEA za ta ci gaba da sanya ido da tantancewa ayyukan da kasar ke aiwatarwa, har zuwa karin watanni 3, karkashin yarjejeniyar fahimtar juna da sassan biyu suka amince.

Har ila yau, yarjejeniyar za ta ba da damar ci gaba da gudanar da sauran shawarwari na siyasa a dukkanin matakai, wadanda za su taimaka wajen kaucewa wani yanayi na tafiya a cikin duhu.

Mr. Grossi ya kara da cewa, a hakikanin gaskiya, hukumarsa ba za ta samu damammaki sosai ba, amma duk da haka, za ta ci gaba da sanya ido da tantance ayyukan da kasar ta Iran ke aiwatarwa. (Saminu Hassan)