logo

HAUSA

Cutar COVID-19 ta yi sanadin rayukan dubban ma’aikatan lafiya a Amurka

2021-02-22 10:06:12 CRI

Shekara guda bayan barkewar annobar COVID-19, adadin mutanen da suka mutu sanadiyyar cutar a Amurka, na gab da zarce 500,000, inda dubban jami’an lafiya ke daga cikin wadanda ta halaka.

Rahoton jaridar USA Today, wanda ya bayyana hakan, ya ruwaito cewa, cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta kasar CDC, ta bada rahoton mutane 409,000 sun kamu da cutar, inda kimanin jami’an lafiya 1,438 suka mutu sanadiyyarta a fadin kasar, duk da cewa, cibiyar ta ce alkaluman nata ba su cika ba.

A cewar wani rahoto da kafar Kaiser mai yada labarai game da kiwon lafiya da jaridar The Guardian suka fitar, adadin jami’an lafiya da suka mutu sanadiyyar COVID-19 a kasar, ya kai 3,000.

Rahoton na jaridar USA Today, ya kara da cewa, jami’an lafiya na ta fama da aiki ba dare ba rana, yayin da ake ci gaba da mutuwa da fama da cutar, lamarin da ya sa suke fuskantar barazanar kamuwa da cutar da kuma rashin samun hutu, ba tare da wata alama dake nuna cutar za ta kawo karshe ba.

Har ila yau, ya ce Amurkawa da dama sun kosa da sanya makarin baki da hanci, inda suka matsu su koma harkokinsu kamar a baya, sai dai wannan abu ne da jami’an lafiya ba sa kaunar ji. (Fa’iza Mustapha)