logo

HAUSA

Abuja: dakarun soji 7 sun rasu a hadarin jirgin sama

2021-02-22 09:46:44 CRI

Abuja: dakarun soji 7 sun rasu a hadarin jirgin sama_fororder_210222-aircrash-Saminu-hoto

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce dakarun ta 7 sun rasa rayukan su, sakamakon hadarin jirgi da ya rutsa da su a jiya Lahadi, a kusa da birnin Abuja, fadar mulkin kasar.

Da yake tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, kakakin rundunar Ibikunle Daramola, ya ce jirgin da sojojin ke ciki mallakar rundunar sojin saman kasar kirar KingAir B350i, ya fado ne lokacin da yake dawowa filin jirgi na Abuja daga birnin Minna na jihar Neja, sakamakon lalacewar inji da ya gamu da ita.

Ibikunle Daramola ya kara da cewa, babban hafsan sojojin saman kasar Oladayo Amao, ya ba da umarnin fara bincike game da aukuwar wannan hadari, yana mai kira ga al’umma da su kwantar da hankalinsu, su jira sakamakon binciken da za a gudanar.

Wata majiya daga cibiyar bincike ta AIB dake Najeriyar, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an riga an gano na’urar nadar bayanai ta jirgin. Cibiyar ta kuma ce daga bayanan da na’urar ta nada, ana iya cewa matukin jirgin bai nemi wani taimakon gaggawa ba. Hakan dai na nufin mai yiwuwa, ya yi fatan sauka a filin jirgin mai nisan mita 400 daga inda jirgin ya fadi. (Saminu Hassan)