logo

HAUSA

Mutane 7 sun mutu a harin ta’addanci a kudu maso yammacin Nijer

2021-02-22 10:26:22 CRI

A kalla mutane 7 ne aka hallaka kana wasu mutanen 3 sun samu munanan raunuka a ranar Lahadi bayan da motar dake dauke dasu ta taka wata nakiya da aka binne a kauyen Dargol dake yankin Gotheye a kudu maso yammacin jamhuriyar Nijer, kusa da kan iyakar kasar Mali da Burkina Faso, a cewar wata majiya mai alaka da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar (CENI).

Tawagar jami’an ofishin shiyya na CENI suna cikin motar yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wannan yankin a lokacin da ake tsaka da gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Nijer a ranar Lahadi.

Kasar ta yammacin Afrika ta jima tana fama da munanan hare haren ta’addanci inda aka shafe shekaru ana kaddamarwa a yankunan kudu maso yammacin kasar daga mayakan ‘yan ta’addan masu alaka da kungiyar Al-Qaeda mai rajin kishin Islama dake yammacin Afrika, da kungiyar Ansar Dine, da sauran kungiyoyin ‘yan tada kayar baya masu alaka.(Ahmad)