logo

HAUSA

Sabuwar majalisar zartarwar Libya ta gudanar da taronta na farko

2021-02-22 10:31:07 CRI

Sabuwar majalisar zartarwar kasar Libya da firaministan kasar, sun gudanar da taro karon farko jiya Lahadi, a babban birnin Tripoli, domin tattauna batun kafa sabuwar gwamnati.

Shugaban majalisar da mataimakansa biyu, sun jaddada muhimmancin zaben mutanen da suka dace da sabuwar gwamnatin, wadanda za su iya jagorantar zaben dake karatowa da tabbatar da adalci da cikakken sulhu a kasar.

Majalisar ta kuma gana da hadaddiyar rundunar sojin kasar, domin tattauna batun sake bude hanyar da ta hada biranen Misurata da Sirte, kamar yadda yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta kasar ta tanada. (Fa’iza Mustapha)