logo

HAUSA

Ministan cikin gidan Libya ya tsallake rijiya da baya a harin Tripoli

2021-02-22 09:59:45 CRI

Ministan cikin gidan gwamnatin kasar Libya mai samun goyon bayan MDD Fathi Bashagha, ya tsallake rijiya da baya a jiya Lahadi, lokacin da wasu ’yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka bude masa wuta, a yammacin birnin Tripoli.

Wata sanarwa da ma’aikatar cikin gidan kasar ta fitar, ta ce ’yan bindigar dake cikin wata mota kirar Toyota mai sulke, sun budewa ayarin motocin Fathi Bashagha wuta da bindiga mai sarrafa kan ta, da misalin karfe 3 na yammaci bisa agogon wurin, lokacin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga gidan sa dake gundumar Janzour.

Sanarwar ta ce, nan take masu tsaron ministan suka budewa ’yan bindigar wuta, suka kuma hallaka daya daga ’yan bindigar tare da cafke 2, yayin da daya daga dogaran ministan ya jikkata.

Ma’aikatar dai ta ce tuni aka dauki matakan shari’a masu nasaba da harin da aka kaiwa minista Bashagha. (Saminu Hassan)