logo

HAUSA

Kasar Sin za ta bada gudunmuwar alluran riga kafi 100,000 ga kasar Namibia

2021-02-20 17:04:33 CRI

Jakadan Kasar Sin a Namibia, Zhang Yiming, ya ce kasarsa za ta bada gudunmuwar alluran riga kafin cutar COVID-19 100,000 ga kasar Namibia.

Tuni dai kasar Sin ta bada gudunmuwar riga kafin ga wasu kasashen nahiyar a yayin da suke kokarin samun alluran, ciki har da Zimbabwe da Jamhuriyar Congo.

Yayin wani taro a ofishin jakadancin Sin dake kasar a ranar Alhamis, Zhang Yiming, ya shaidwa uwar gidan shugaban kasar, Monica Geingos cewa, Sin ta yanke shawarar bada fifiko ga kasashe masu tasowa 53 ciki har da Namibia, wajen samun alluran kasarta. (Fa’iza Mustapha)