logo

HAUSA

Sin ta yi jiyyar dimbin sojojin Indiya da aka bar su baya cikin rigingimun bangaren biyu

2021-02-20 16:24:12 CRI

Sin ta yi jiyyar dimbin sojojin Indiya da aka bar su baya cikin rigingimun bangaren biyu_fororder_微信图片_20210220162350

Bayan barkewar rikici a yankin kwarin kogi na Gallevan tsakanin kasashen Sin da Indiya a watan Yunin bara, Sin ta yi jiyya tare da kulawa da sojojin Indiya da aka bari a baya, inda kuma ta mayar da su tare da makamansu zuwa kasar Indiya.

A watan Yunin shekarar 2020, sojojin Indiya suka tsallake layin iyakar kasarsu da Sin, inda suka kafa tantunansu a bangaren kasar Sin. Duk da gargadin da kwamandan rajamanti na rundunar tsaron iyakokin kasar Sin, Qi Fabao ya yi, kan tanadin sulhu da aka yi a baya, Indiya ta yi biris, ta girke dimbin sojojinta a wurin, inda suka kai hari ba zato ba tsammani kan kwamandan na Sin da sojojinsa.

Da ganin hakan, rundunar sojin kasar Sin ta dauki matakin da ya wajaba don mai da martani. Indiya ta sanar da rasuwar sojojinta 20, Sin kuma ta rasa sojoji 4 yayin da kwamandan rajamanti daya ya ji rauni.

Sai dai, kafofin yada labarai na Indiya da sauran hukumomin leken asiri na kasashen yamma, sun ce sojojin Sin fiye da 10 ne suka rasu, kuma sojojin Indiya sun cimma nasarar dakile dakarun kasar Sin. Wannan labari karya ne kwata-kwata.

Rahotanni sun bayyana cewa, Indiya ta bar dimbin sojojinta wadanda suka ji rauni a filayen kasar Sin, amma Sin ta yi jiyyarsu tare da mayar da  su gami da makamansu gida.

Abin lura shi ne, bayan barkewar rikici a yankin kwarin kogi na Gallevan, duk da kofofin yada labarai na Indiya sun shafa bakin fenti kan kasar Sin, Sin ta yi hakuri ba ta mai da martani ba, don bayyana niyyarta na kiyaye dangantakar kasashen biyu da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Sin ta gabatar da hakikanin halin da ake ciki a wancan lokaci bayan Indiya ta karawa lamarin gishiri ta baiwa sojojin da suka shiga yankin kasar Sin ba bisa doka ba, lambar yabo ta jaruman Gallewan. (Amina Xu)