logo

HAUSA

Sakatare Janar na MDD ya jinjinawa matakin Amurka na komawa yarjejeniyar sauyin yanayi ta birnin Paris

2021-02-20 17:05:41 CRI

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yabawa matakin Amurka na sake komawa yarjejeniyar sauyin yanayi ta birnin Paris, yana mai kira ga duniya, ta dauki matakin tabbatar da kawar da fitar da sinadarai masu gurbata muhalli kawo shekarar 2050.

A ranar 22 ga watan Afrilun 2016 ne, Amurka ta rattaba hannu kan yarjejeniyar, ta kuma bayyana amincewarta ga tanade-tanadenta a ranar 3 ga watan Satumbar shekarar. Sai dai, jim kadan bayan darewar tsohon shugaban kasar Donald Trump kan karagar mulki, Amurka ta sanar da niyyarta ta janyewa daga yarjejeniyar a watan Yunin 2017. A kuma ranar 4 ga watan Nuwamban bara ta janye a hukumance.

A ranarsa ta farko a fadar White House, sabon shugaban Amurka Joe Biden, ya rattaba hannu kan sabon daftarin amincewa da yarjejeniyar, wadda aka mikawa Sakatare Janar na MDD a ranar, matakin da ya ba Amurkar damar sake kasancewa cikin yarjejeniyar a ranar 19 ga watan nan na Fabrairu. (Fa’iza Mustapha)