logo

HAUSA

Ngozi Okonjo Iweala: Ra’ayin kishin kasa a fannin nazari da raba allurar rigakafin cutar COVID-19 yana ja da aikin dakile yaduwar annoba baya

2021-02-19 14:09:56 CRI

Ngozi Okonjo Iweala: Ra’ayin kishin kasa a fannin nazari da raba allurar rigakafin cutar COVID-19 yana ja da aikin dakile yaduwar annoba baya_fororder_2

Sabuwar babbar darektar kungiyar cinikayyar duniya ta WTO Ngozi Okonjo Iweala ta yi gargadi cewa, bai dace a yi amfani da ra’ayin kishin kasa a yayin da muke aiwatar da aikin nazari da raba allurar rigakafin cutar COVID-19, domin matakin zai mayar da aikin dakile yaduwar cutar a duk fadin duniya baya, da haddasa hasarar tattalin arzikin kasashen duniya.

Ta kara da cewa, abu na farko da za ta mayar da hankali, bayan ta kama aikin jagorancin kungiyar WTO, shi ne tabbatar da ganin kungiyar WTO ta samar da karin gudummawa wajen yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19. Ta ce, ya kamata mambobin kungiyar su gaggauta ayyukan kawar da takunkumin da suka kakaba game da fitar da kayayyaki da magungunan da ake bukata don yaki da cutar. (Maryam)