logo

HAUSA

UNICEF ya yi kira da a gaggauta sakin yaran da aka sace a Najeriya

2021-02-18 19:09:51 CRI

Asusun tallafawa kananan yara na MDD (UNICEF) ya yi kira a hanzarta sakin yaran da aka yi amannan ‘yan bindiga ne suka sace su, a yankin arewa maso tsakiiyar Najeriya ba tare da gindaya wani sharadi ba.

Wata sanarwa da wakilin UNICEF a Najeriya Peter Hawkis, ya aikawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua Alhamis din nan, ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin da ‘yan bindigan suka kai, kana ya yi kira a dawo da yara ga iyayensu lami lafiya.(Ibrahim)