Direbar jirgin kasa ta farko a Najeriya: Kamfanonin kasar Sin sun canja rayuwar ’yan Najeriya
2021-02-08 16:05:14 CRI
“Abin sha’awa ne zama mace ta farko mai tuka jirgin kasa a Najeriya. Ina alfahari da haka, aikin da mutane su kan ce, mata ba za su iya yi ba. Kamfanin kasar Sin ya canja rayuwata.”
Issah Fatima Abiola, ’yar kasar Najeriya. Ta fara aiki a kamfanin CCECC a shekarar 2008, da farko an dauke ta a matsayin mai ba da taimako a ofishin sashen shimfida hanyoyin layin dogo. Daga baya, kamfanin ya horas da ita don zama mace ta farko mai tuka jirgin kasa a Najeriya. A cewarta, albashinta ya karu daga Naira dubu 50 zuwa Naira dubu 130 a kowane wata, abin da ya karfafa mata gwiwa da kula da iyalanta da biyan kudaden yau da kullum.
Bayanai na cewa, a da layin dogo a Najeriya ya fi na sauran kasahen Afrika yawa, amma babu a sabon babban birnin kasar Abuja, kuma tsoffin layukan dogo ba su da inganci, kuma tsarinsu ba daya ba ne, abin da ya sa mazauna wurin ke fuskantar wahalar zirga-zirga. Mataimakin manajan sashen kula da ayyukan da CCECC ya gina a Najeriya Guo Chen ya ce, nasarar da aka cimma wajen amfani da layin dogo tsakanin Abuja da Kaduna, ya yayata fasahar kasar Sin a fannin layin dogo dake tsakanin Lagos da Ibadan da kuma layin dogo dake ratsaa yankunan tsakiyar kasar. Wannan layi dogo yana cike da salo iri na kasar Sin, wato Sin ta zuba kudade wajen gina shi da ba da taimakon gina shi kuma samar da na’urori da jirage da tsarin gudanar da harkokinsa. Guo ya ce:
“Yayin da ake aikin gina wannan layin dogo, an samar da guraben aikin yi 4000 kai tsaye, yanzu a kan samar da guraben aikin yi fiye da 800 don gudanar da harkoki dake da nasaba da shi a yau da kullum. Haka kuma an kara inganta kwarewar ma’aikatan wuri ciki hadda Issah. Matakin da ya kyautata yanayin zirga-zirgar kasar, da raya tattalin arziki da al’ummar kasar. Gwamnatin kasar Sin ta samar da rancen kudi mai rangwame wajen gudanar da aikin, kazalika kamfaninmu ya sauke nauyin dake wuyansa na raya al’umma, wato horas da ma’aikata da koyar da kimiya da fasaha, da ma gina hanyoyi da makarantu kyauta, abubuwan da suka bayyana mutuncin kasar Sin.”
Babatunde Lawal, wani fasinja ne da ya kan yi amfani da layin dogo dake tsakanin Abuja da Kaduna, game da wannan layin dogo ya ce:
“Wannan layin dogo ya rage lokacin tafiya tsakanin Abuja da Kaduna, abin da ya saukaka mana tafiye-tafiye, mutane da dama suna kai komo a tashar Idu. Baya ga inganta zirga-zirga, layin dogo ya kuma samar da dimbin guraben aikin yi. Wannan kasuwar dake waje da tashar, tana da wadata matuka. Wata gada ce dake hada wadannan birane biyu, kuma wata alama ce ta zumuncin Najeriya da Sin.”
A matsayinta na mai tuka jirgin kasa tsakanin Abuja da Kaduna da kuma a cikin birnin Abuja, Issah tana da kyakkyawar mu’amula da ma’aikatan Sinawa, ta ce, “ina matukar farin cikin yin aiki tare da ma’aikatan Sinawa, sun koya min Sinanci, na ci gajiya matuka.” Ban da wannan kuma, ta zabi wani sunan na Sinanci wato “Bai Yang”, ta ce:
“Lokacin da na kai ziyara a kasar Sin a karon farko, na ga itacen Populus wato Bai Yang da Sinanci, shi ya sa na yanke shawarar zabar sunan a matsayin sunana na Sinanci.”
A kasar Sin, itacen Populus yana alamta ruhin magance wahalhalu da kokarin samun ci gaba. Issah wadda ta shafe shekaru 13 tana aiki tare da Sinawa, ta ga yadda Sinawa ke kokarin magance duk wata wahala don taimakawa Najeriya wajen shimfida layin dogo da kafa tashoshin jiragen sama, tana godiya matuka ga ayyukan da kamfanonin kasar Sin yake yi. Ta ce:
“Layin dogo dake tsakanin biranen Abuja da Kaduna, ya samar da guraben aikin yi da yawa ga matasan Najeriya. Ban da wannan kuma, ana matakan tsaro da saukin tafiye-tafiye. Ban da wadannan layin dogon da kamfanonin kasar Sin suka gina, akwai kuma tasoshin jiragen sama da CCECC ya gina da jiragen kasa samfurin DMU da na fi sha’awa.”
A shekarar 1971, Sin da Najeriya suka kulla dangantakar diplomasiyya tsakaninsu, a cikin wadannan shekaru 50 da suka gabata, Sinawa da kuma kamfanonin kasar Sin da dama, sun je wannan kasa, sun ba da taimakon gina wasu manyan ababen more rayuwa ciki hadda layin dogo dake tsakanin biranen Abuja da Kaduna, da layin dogon dake tsakanin biranen Lagos da Ibadan, da layin dogo dake dab da bakin teku, layin dogo dake cikin birnin Abuja da tasoshin jiragen sama da dama da madatsar ruwa ta Zungeru da yankin ciniki cikin ’yanci na Lekki, ma’aikatan kamfanonin kasar Sin tamkar itacen Populus ne, wadanda suke kokarin gina manyan ababen more rayuwa a Najeriya, don kyautata rayuwar al’ummar kasar. Saboda haka, mazauna wurin sun amince da gudunmawar da suka bayar. Rayuwar mutane da dama ciki hadda Issah Fatima Abiola ta kyautatu. Issah ta yaba cewa:
“Ina godiya sosai ga gwamnatin kasar Sin, ina godiya sosai ga kamfanin CCECC.” (Amina Xu)