logo

HAUSA

Bach: Kasar Sin a shirye take wajen karbar kwararrun 'yan wasan kasashe daban daban

2021-02-06 16:10:17 CRI

Yayin da ya rage shekara guda a kaddamar da wasannin Olympics na lokacin hunturu na shekarar 2022 a birnin Beijing na kasar Sin, shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya, Thomas Bach, ya aike da wani sakon taya murna ga shugaban babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin Mista Shen Haixiong, inda Bach ya jaddada cewa, ko da yake annobar COVID-19 ta haifar da kalubale mai yawa, ana da imani sosai, cewar kasar Sin ta riga ta shirya, don karbar kwararrun 'yan wasan kasashe daban daban, masu gudanar da wasanni na lokacin hunturu.

Bach ya waiwayi hirar da ya yi da shugaban kasar Sin Xi Jinping a kwanakin baya, inda ya ce, shugaban na kasar Sin ya ziyarci dakunan da aka gina da yi wa kwaskwarima, kuma ya fahimci cewa, za a gudanar da wasannin Olympics na lokacin hunturu a Beijing cikin nasara. A cewar Bach, shi da shugaba Xi Jinping dukkansu sun yarda cewa, ya kamata a yi watsi da sabanin ra’ayi a fannin siyasa, sa'an nan a girmama wasannin Olympics. (Bello Wang)

Bello