Za a wallafa bayanin da Xi Jinping ya rubuta kan kare ikon mallakar fasaha
2021-01-31 20:27:11 CRI
An ce za a wallafa wani bayanin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubuta, game da batun kare ikon mallakar fasaha da kuma karfafa mahimmancin kirkire-kirkire don inganta aikin gina wani sabon salon raya kasa, a gobe Litinin.
Bayanin na shugaba Xi, za a buga shi ne a mujallar Qiushi wallafa ta uku ta wannan shekarar. (Bello Wang)
