logo

HAUSA

Sin ta bukaci Amurka da ta daina aika mummunan sako ga ‘yan awaren Taiwan

2021-01-25 19:59:58 CRI

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bukaci Amurka da ta daina aika mummunan sako ga ‘yan aware dake neman ‘yancin yankin Taiwan na kasar Sin.

Da yake amsa tambayar da aka yi masa game da kalaman da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi, inda ta bukaci babban yankin kasar Sin da ya daina matsawa yankin na Taiwan lamba, Zhao Lijian ya jaddada cewa, matsayin kasar Sin game da yankin na Taiwan bai sauya ba, kuma a fili yake.

Zhao ya ce, kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma Taiwan, wani bangare na kasar Sin da ba za a iya raba shi ba. A don haka, a shirye kasar Sin take ta kare ‘yanci da yankunanta, za kuma ta sanya kafar wando guda da duk wasu ‘yan aware masu neman ‘yancin Taiwan, da masu neman yi mata kutse daga ketare.

A don haka, ya bukaci Amurka, da ta martaba manufar kasar Sin daya tak a duniya, da kuma sanarwowin hadin gwiwa guda uku da kasashen biyu suka sanyawa hannu, ta kuma rika yin kaffa-kaffa kan harkokin da suka shafi Taiwan, don kaucewa lalata alakar dake tsakanin Sin da Amurka, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Taiwan.(Ibrahim)