logo

HAUSA

Dabarun gwamnatin Sin ya baiwa duniya kwarin gwiwar tinkarar kalubaloli

2021-01-25 16:59:50 CRI

Dabarun gwamnatin Sin ya baiwa duniya kwarin gwiwar tinkarar kalubaloli_fororder_0125-1

“Abin da babba ya hanyo yaro ko ya hau kololuwar bishiyar rimi ba zai iya hange ba.” A lokuta da dama, shugabanni da masanan kasa da kasa suna martaba kalamai ko ra’ayoyin da shugaban Sin Xi Jinping ke gabatarwa a yayin muhimman tarukan kasa da kasa ta yadda kamalan suke zama tamkar abin da malam Bahaushe ke cewa, “mikiya mai hangen nesa.” Sau da dama ana daukar kalaman shugaban a matsayin wata hikima ko dabara dake iya taimakawa duniya wajen kokarin cire kitse daga wuta game da kalubalolin dake addabar duniya. Idan za a iya tunawa, a watan Janairun shekarar 2017, Xi Jinping ya taba yin cikakken bayani game da ra’ayin samar da makomar bai daya ga dukkan bil Adama yayin wani taron MDD da aka gudanar a birnin Geneva, wannan ita ce dabarar da Xi ya gabatar game da yadda za a fuskanci babban kalubalen duniya. Yanzu, shekara daya ke nan da ake fama da yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, ra’ayin da Xi ya gabatar ya ba da amsa ga kasa da kasa game da yadda za a fuskanci wannan matsala. Koda a shekarar da ta gabata ma, shugaban na kasar Sin ya yi ganawa da kuma yin shawarwari har sau 87 ta yanar gizo tare da shugabannin kasashen duniya da na hukumomin kasa da kasa, da halartar taruka na musamman game da yaki da annobar a tsakanin bangarori daban daban kimanin 22, kamar babban taron hukumar kiwon lafiyar duniya, da taron kolin shugabannin kungiyar G20 game da yaki da cutar COVID-19 da sauransu. Lamarin da ya ba da jagoranci ga kasa da kasa ta fuskar aikin yaki da annobar cutar COVID-19. Ban da haka kuma, kasar Sin ta gudanar da aikin ba da taimakon jin kai ga kasashe da dama a shekarar 2020, inda ta samar da abin rufe hanci da baki sama da biliyan dari 2, da rigunan kariya sama da biliyan 2, da kuma na’urorin gwajin kwayoyin cutar COVID-19 miliyan 800 ga kasashe da dama. Ta kuma ba da taimakon yaki da cutar ga kasashe sama da 150 da kungiyoyin duniya 10, baya ga aika tawagogin ma’aikatan lafiya 36 zuwa kasashe 34 dake da bukata. Haka kuma, a matsayinta na kasar dake kan gaba a aikin nazarin allurar riga-kafin cutar COVID-19, kasar Sin ta kafa cibiyar nazarin allurar riga-kafin COVID-19 ta kasashen BRICS. A halin yanzu, ban da kasashen Brazil, Indonesiya, Masar da Turkiya da sauransu, akwai karin kasashe masu tasowa da suka samu allurar riga-kafi daga kasar Sin. Ko shakka babu, ra’ayin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga dukkanin bil Adama na ci gaba da samun amincewa tsakanin kasashen duniya, har ma an shigar da ra’ayin cikin muhimmiyar takardar MDD.

Shin ko ta yaya za a fuskanci manyan kalubalolin dake gaban duniya bayan kawar da wannan annoba? Amsar ita ce, yin kokarin raya makomar bai daya ga daukacin bil-Adama, kuma wannan ita ce shawarar da mahukuntan Sin suka jima suna gabatarwa duniya. “Dabara dai ta rage ga mai shiga rijiya.” (Ahmad Fagam)