logo

HAUSA

Wasu hare-hare sun yi sanadin mutuwar sojojin Mali 6

2021-01-25 09:49:41 CRI

An kashe sojojin Mali 6, a wasu hare-hare da aka kai kan sansanonin soji 2 dake yankin tsakiyar kasar a jiya Lahadi.

Wata sanarwar da rundunar sojin Mali ta fitar, ta ce an kai hari kan sansanoni 2 na sojojin kasar a yankunan Boulkessi da Mondoro a jiya da safe, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojoji 6 da jikkatar wasu 18.

Sanarwar ta ce sojojin sun mai da martani kan hare-haren biyu da aka kai a lokaci guda, inda suka kashe ’yan ta’adda 30, tare da kwato Babura kimanin 40 da wasu manyan makaman soji.

Kawo yanzu dai, babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai hare-haren.

Hari na baya da aka kai sansanonin soji biyu a Boulkessi da Mondoro dake kan iyakar kasar da Burkina Faso a ranar 30 ga watan Satumban 2019, ya yi sanadin mutuwar sojojin Mali 40. Kuma Kungiyar Jama'at Nusrat al-Islam wa al-Muslimeen ce ta dauki alhakin kai harin na wancan lokaci. (Fa’iza Mustapha)