logo

HAUSA

AU ta yi maraba da fara aikin yarjejeniyar haramta amfani da makaman nukiliya

2021-01-24 15:18:14 CRI

Hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika AU ta yi maraba da fara amfani da yarjejeniyar haramta amfani da makaman kare dangi.

Cikin sanarwar da shugaban gudanarwar AU, Moussa Faki Mahamat ya fitar, ya ce yana maraba da shigar AU cikin yarjejeniyar haramta amfani da makaman nukiliya ta TPNW.

Sanarwar ta ce, shugaban kungiyar ta Afrika mai mambobin kasashe 55, ya ce wannan mataki ne mai cike da tahiri ga duniya, inda ya jaddada aniyar AU wajen cimma nasarar raba duniya da makaman kare dangi.

Mahamat ya bayyana cewa, yarjejeniyar wata muhimmiyar gudunmawa ce wacce za ta tabbatarwa duniya zaman lafiya da tsaro ta hanyar kawar da makaman nukiliyar daga doron kasa.

Mahamat ya taya mambobin kasashen AU murnar amincewa da yarjejeniyar, kana ya bukaci bangarorin da ba su amince da yarjejeniyar ba da su gaggauta amincewar.

Ya kuma jaddada aniyar hukumar AU wajen goyon bayan mambobin kasashen kungiyar domin sauke nauyin dake bisa wuyansu don cimma muradun samar da zaman lafiya da tsaron Afrika, kamar yadda ke kunshe cikin ajandar neman dawwamamman ci gaban nahiyar nan da shekarar 2063.(Ahmad)