logo

HAUSA

Masanin Sudan: CPC tana da kwarewar shugabanci

2021-01-24 16:56:08 CRI

Wani masanin siyasar kasar Sudan ya bayyana kwarin gwiwa game da kwarewar da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC ke da ita wajen ci gaba da inganta tsarin shugabanci bisa amfani da salon kwarewar da take da shi, ta cimma manyan nasarorin bunkasa tattalin arziki da zaman rayuwar al’umma, kana ta kyautata yin sauye sauye da bude kofa.

Abdul-Khaliq Mahjoub, wani shehin malami ne a fannin siyasa a cibiyar nazarin kimiyyar siyasa dake Khartoum, ya ce shekarar 2021 ta yi daidai da cika shekaru 100 da kafuwar JKS, kuma ya kasance wani muhimmin lokaci bisa lura da irin rawar da jam’iyyar ta taka, ba wai ga kasar Sin kawai ba har ma ga duniya baki daya.

Ya ce a cikin shekaru 100 da suka gabata, jam’iyyar CPC ta yi nasarar jagorantar kasar Sin wajen kaiwa matakai daban daban na ci gaba da samun makoma mai haske ta hanyar wasu ingantattaun tsare tsare masu alfanu.

Mahjoub ya bayyana kwarewar da jam’iyyar CPC ta nuna a yaki da annobar COVID-19 a matsayin wata hujja dake kara tabbatar da karfin da jam’iyyar ke da shi wajen tinkarar manyan batutuwa.

“Tun bayan barkewar annobar, jam’iyyar ta yi ta kokarin zaburar da rassanta dake yankunan kasar domin taimakawa shirin dakile annobar da kuma karfafawa Sinawa gwiwa don kawar da annobar COVID-19," in ji masanin.(Ahmad)