logo

HAUSA

Sharhin Xinhua: Sanarwar Pompeo hasarar takardu ne kawai

2021-01-22 12:44:11 CRI

A ranar Talata ne tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya bada sanarwa da sunan ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka, inda ya sake yin suka game da manufofin jahar Xinjiang ta kasar Sin, kana ya yi yunkurin yin shisshigi a harkokin cikin gidan kasar Sin ta hanyar fakewa da hakkin dan adam.

Wannan yunkuri ne na nuna adawa ga kasar Sin da nufin cusa kiyayya a tsakanin kananan kabilun dake jahar Xinjiang, da kokarin lalata zaman lafiyar yankin kana da yada bayanai marasa tushe ga al’ummar duniya da sunan biyan bukatu na siyasa game da manufofin kasar Sin.

An riga an bayyanawa duniya hakikanin bayanai game da jahar Xinjiang tare da gabatar da sahihan alkaluma da misalai. A halin yanzu, kasar Sin ta riga ta fitar da takardun bayanai kimanin guda takwas game da batutuwan dake shafar yankin Xinjiang, kana gwamnatin jahar Xinjiang Uygur mai cin gashin kai ta gudanar da tarukan manema labarai sama 20 domin bayyana hakikanin halin da ake ciki.

Sukar da Pompeo yake yiwa kasar Sin ba zai taba yaudarar al’ummar duniya ba, kuma ba zai taba yin tasiri wajen zubar da kimar kasar Sin ko kuma lalata ci gaban kasar Sin ba. (Ahmad Fagam)