logo

HAUSA

Hadin gwiwar Sin da Afrika kan yaki da COVID-19 na kara fadada

2021-01-22 12:03:50 CRI

Wani masanin harkokin tattalin arziki na kasar Habasha, Costantinos Bt. Costantinos ya ce hadin gwiwar Sin da Afrika wajen yaki da annobar COVID-19 dake ci gaba da bazuwa na da fadi sosai.

Costantinos Bt. Costantinos, wanda kuma mashawarci ne ga Tarayyar Afrika AU da hukumar kula da tattalin arzikin Afrika ta MDD (ECA), ya shaidawa wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, zuwa yanzu dangantakar bangarorin biyu kan yaki da COVID-19 na kara fadada sosai.

A cewarsa, kayayyakin lafiya da Sin ta turawa kasashen nahiyar Afrika, sun yi matukar taimakawa kasashenta, inda ya ce kusan dukkan kasashen sun samu kayayyakin tallafi da suka dace, wadanda suka hada da magungunan yaki da cutar.

Ya kara da cewa, yayin da take kula da al’ummarta, Sin na kan gaba wajen taimakawa kasashen Afrika wajen tunkarar tasirin annobar. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha