logo

HAUSA

Jarin da Sin ta zuba kai tsaye a ketare a shekarar 2020 ya karu da 3.3%

2021-01-22 13:39:41 CRI

Jarin da Sin ta zuba kai tsaye a ketare a shekarar 2020 ya karu da 3.3%_fororder_aaa

Kididdigar da ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin da hukumar kula da musayar kudade ta kasar Sin suka fitar ta nuna cewa, a shekarar 2020, jarin da kasar Sin ta zuba kai tsaye a kasashen ketare ya kai dallar Amurka biliyan 132.94, adadin da ya karu da 3.3%. Kana jarin da kasar ta zuba a fannonin da ba su shafi sha’anin kudi ba, ya kai dallar Amurka biliyan 110.15. Hadin gwiwar Sin da kasashen ketare a fannin zuba jari tana bunkasa yadda ya kamata. Haka kuma jarin da kasar Sin take zubawa a kasashen ketare yana karuwa sosai.

A sa’I daya kuma, sana’ar hayar ma’aikata don su samar da hidima tana bunkasa cikin yanayi mai kyau, inda jimlar kudin da aka samar a fannin hayar ma’aikata daga kasar Sin don su samar da hidima ta zarce dallar Amurka biliyan dari.

Kakakin ma’aikatar harkokin kasuwancin kasar Sin Gao Feng ya bayyana cewa, kasar Sin ta inganta harkokin zuba jari da hadin gwiwa da kasashen dake cikin shawarar “Ziri daya da hanya daya” kamar yadda ake fata a shekarar 2020.

An kuma gabatar da bayanai kan yanayin sana’ar hayar ma’aikata don su samar da hidima na shekarar 2020. Inda a wannan shekara, Sin ta kara samun karbuwa a kasuwannnin kasa da kasa ta fuskar wannan aiki, jimlar kudi da aka samar a wannan fanni, ta zarce dallar Amurka biliyan dari, lamarin da ya sa, adadin hidimar da Sin take sayarwa a ketare ya karu da 3.8%. (Maryam)