logo

HAUSA

Kakakin Sin: Pompeo ne ya jawo kansa takunkumin da aka sanya masa

2021-01-22 09:40:42 CRI

Mai magana da yawun harkokin yankunan Hong Kong da Macao na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya ce ya goyi bayan matakin sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta dauka jiya Alhamis, na kakabawa wasu Amurka 28 takunkumi, ciki har da tsohon sakataren wajen kasar Mike Pompeo, saboda yadda ya keta ’yancin kasar ta Sin.

Da yake karin haske cikin wata sanarwa, jami’in ya ce, yadda Pompeo yake tsoma baki a harkokin yankin Hong Kong, da shafawa tsarin kasa daya, tsarin mulki biyu na kasar Sin bakin fenti, da kitsawa da sanya mata takunkumi babu gaira babu dalili, duk sun keta dokokin kasa da kasa da ka’idojin hadin gwiwar kasa da kasa. Haka kuma matakin nasa, ya illata alakar Sin da Amurka, da haifar da zagon kasa ga makoma da ma zaman lafiyar yankin Hong Kong.

Sanarwar ta kara da cewa, tarihi ya tabbatar da cewa, duk wasu makiyan kasar Sin dake kokarin tsoma baki a cikin gidanta, ba za su yi nasara ba. A don haka, sanarwar ta gargadi duk wani mai kokarin tsoma baki a harkokin yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, to, hakarsa ba za ta cimma ruwa ba. (Ibrahim)