logo

HAUSA

Alkaluman hauhawar farashin kayayyaki a Afirka ta kudu sun ragu sosai

2021-01-21 10:28:15 CRI

Rahotanni daga kasar Afirka ta kudu na nuna cewa, alkaluman farashin kayayyakin kasar na shekarar 2020, ya tsaya kan kaso 3.3 cikin 100, wanda ke nuna hauhawar farashin kayayyaki mafi kankanta da kasar ta samu tun shekarar 2014.

Alkaluman hukumar kididdigar kasar (Stats SA) sun danganta bangaren abinci da abubuwan sha wadanda ba su shafi barasa ba, a matsayin jigon hauhawar farashin kayayyaki a kasar a watan Disamba, inda aka samu karuwar kaso 0.5 cikin 100 a kowa ne wata, da karuwar kaso 6.0 a shekara. An dai fara samun karuwar hauhawar farashin ne tun daga watan Nuwamba, inda har ya kai kaso 5.8 cikin 100

A yayin da babban bankin kasar yake shirya fitar da sanarwa game da mizanin kudin ruwa a yau, watakila, ko raguwar farashin kayan, za ta sa kwamitin tsara manufofin kudin kasar yanke shawara kan matakin da ya dace dauka.

Shugaban sashen nazarin tattalin arzikin da kimiyar kasuwanci a jami’ar Witwatersrand, Jannie Rossouw, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, babban bankin kasar, yana duba hauhawar farashin da za a iya samu a nan gaba.  Don haka, idan matsalar ta ragu aka kuma tallafa, sannan ya tsaya a haka, to, yana iya shafar shawarar da banckin zai yanke. Amma, idan har ana zaton matsalar za iya karuwa cikin watannin mazu zuwa, to, bankin ba zai sauya mizanin kudin ruwan ba.(Ibrahim) 

Bello