logo

HAUSA

Alluran riga kafin CNBG na kasar Sin zai yi tasiri a kan nau’o’in COVID-19

2021-01-21 09:50:28 CRI

Mataimakin shugaban kamfanin harhada magunguna na CNBG reshen Sinopharm na kasar Sin Zhang Yuntao ya bayyana cewa, alluran riga kafin COVID-19 da kamfanin ya samar, yana iya tasiri kan nau’o’in kwayar cutar COVID-19 daban-daban

Da yake Karin haske yayin wani taron manema labarai da aka shirya, jami’in ya bayyana cewa, kamfanin ya tattaro samfuran kwayoyin cutar COVID-19 da aka gano a wasu kasashe a karshen 2020, ya kuma gudanar da gwaje-gwaje a kansu.

Yana mai cewa, sakamakon binciken da aka gudanar ya nuna cewa, allurar riga kafin tana iya ba da kariya ga nau’o’in kwayar cutar a ko’ina a duniya. Koda yake, sun gano wani rahoto kan wasu nau’o’in kwayar cutar, tun lokacin da aka gano su a wasu kasashe, ciki har da Afirka ta kudu da Burtaniya da Najeriya.  Ya kara da cewa, kamfanin yana mayar da hankali kan sauye-sauyen da za a iya samu, zai kuma ci gaba da gudanar da gwaje-gwaje kan mabanbantan nau’o in kwayar cutar.(Ibrahim)

Bello