logo

HAUSA

Kyautata alakar Sin da Amurka zai taimakawa gwamnatin Biden wajen shawo kan manyan kalubale

2021-01-21 15:34:50 CRI

Kyautata alakar Sin da Amurka zai taimakawa gwamnatin Biden wajen shawo kan manyan kalubale_fororder_A

Kamar yadda muka sani, shugaban Amurka na 46 Joe Biden, ya sha rantsuwar kama aiki a ranar 20 ga watan Janairun nan. Kuma tuni ya shaidawa duniya aniyarsa, ta shawo kan manyan kaulbale da Amurka ke fuskanta, ciki har da yaki da annobar COVID-19 da ta yiwa kasar kamun kazar kuku, baya ga batun rashin daidaito tsakanin sassan al’ummun kasar, da batun sauyin yanayi, da ma rawar da Amurkar ke takawa a harkokin kasa da kasa.

Kalaman da shugaba Biden ya yi, yayin da ya sha rantsuwar kama aiki, na nuna aniyar sa ta hade kan Amurkawa, da gyara irin barnar da tsohon shugaban kasar Donald Trump ya tafka, musamman a fannin alakar kasar da sauran sassan kasa da kasa.

Ko shakka ba bu, an rantsar da Mr. Biden a wani lokaci da Amurka ke fuskantar mummunan sakamakon ayyukan da gwamnatin Trump ta aikata. Sai dai a daya bangaren kuma, Mr. Biden ta fara aikin magance wasu daga kura kuren da tsohuwar gwamnatin ta Trump ta aiwatar, musamman batun mayar da kasar cikin yarjejeniyar sauyin yanayi ta Faris, da hukumar lafiya ta WHO, da dage takunkumin hana wasu al’ummun kasashen musulmi shiga Amurka.

Kyautata alakar Sin da Amurka zai taimakawa gwamnatin Biden wajen shawo kan manyan kalubale_fororder_B

Daya daga bangarorin da ake hasashen gwamnatin Biden za ta yi rawar gani shi ne, dawo da kyakkyawar alakar dake tsakanin Amurka da Sin, musamman ma batun kawar da haraji kala kala da tsohuwar gwamnatin Trump ta rika sanyawa hajojin Sin dake shiga Amurka, da yiwa kamfanonin Sin matsin lamba ba gaira ba dalili.

Game da hakan, dandalin nazarin harkokin kasuwanci tsakanin Sin da Amurka da hadin gwiwar cibiyar lura da harkokin tattalin arziki ta Oxford, sun fitar da wani rahoto, wanda ya nuna cewa, saukaka haraji ga hajojin Sin da ake shigarwa Amurka kadai, na iya taimakawa Amurka farfado da tattalin arzikin ta, zai kuma fadada guraben ayyukan yi da take fatan samarwa al’ummun ta, a gabar da ake ci gaba da tunkarar manyan kalubale da cutar COVID-19 ta haifarwa kasar.

Idan an yi la’akari da wannan rahoto, da ma sauran hasashe da masana ke yi, za a ga cewa, hadin gwiwa da fahimtar juna tsakanin Sin da Amurka, musamman a wannan gaba da Amurkar ta samu sabon jagoranci, zai taimakawa sabuwar gwamnatin Biden din shawo kan manyan kalubalen dake gabanta. Har ila yau, sassan biyu za su samu sabon zarafi na tunkarar kalubalolin dake addabar duniya cikin hadin gwiwa.(Saminu Alhassan)