logo

HAUSA

Africa CDC ta fara shirin odar rigakafin COVID-19 ga kasashen AU 55

2021-01-21 09:56:04 CRI

Jiya Laraba hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta Afrika CDC, ta sanar da shirin fara yin odar alluran rigakafin cutar COVID-19 ga dukkan mambobin kasashen kungiyar tarayyar Afrika AU.

Wannan yunkuri ne na sashen rarraba magunguna na Afrika wato AMSP, a madadin hukumar ta Africa CDC, matakin na zuwa ne mako guda bayan sanarwar da shugaban kasar Afrika ta kudu, kana jagoran kungiyar tarayyar Afrika AU, Cyril Ramaphosa, ya fitar a ranar 14 ga watan Janairu cewa, AU ta samu kashin farko na alluran rigakafin cutar COVID-19 miliyan 270 karkashin shirin tawagar samar da rigakafin COVID-19 na Afrika wato AVATT.

Sanarwar da Afrika CDC ta fitar ta ce, sashen raba alluran na AMSP, a madadin Africa CDC, zai fara shirin odar rigakafin ga dukkan mambobin kasashen AU.

Bankin shigi da ficin kasuwanci na Afrexim, shi ne zai jagoranci biyan kudaden rigakafin wanda kudin ya kai sama da dala biliyan 2, inda zai biya kamfanonin a madadin mambobin kasashen.

A cewar Africa CDC, shirin ya tanadi wani tsarin raba daidai na rigakafin cutar ta COVID-19 ga mambobin kasashen AU 55.(Ahmad)