logo

HAUSA

Masar da Qatar za su maido da huldarsu bayan shafe sama da shekaru 3 suna takaddama

2021-01-21 08:57:42 CRI

A ranar Laraba kasashen Masar da Qatar suka amince za su sake ci gaba da yin huldar diflomasiyya bayan shafe sama da shekaru uku suna zaman tankiya a tsakaninsu, ma’aikatar harkokin wajen Masar ne ta bayyana hakan cikin wata sanarwa.

Sanarwaar ta kara da cewa, an dauki wannan mataki ne bayan wata yarjejeniyar fahimtar juna ta Al-Ula, wacce bangarorin suka sanyawa hannu a lokacin taron kolin majalisar hada kan kasashen yankin Gulf karo na 41 wanda aka gudanar a kasar Saudi Arabia.

Ita dai yarjejeniyar ta Al-Ula ta cimma matsayar kawo karshen kauracewar da kasashen Larabawa suka yiwa Qatar, da suka hada da kasashen Masar, Saudi Arabia, Hadaddiyar daular Larabawa da Bahrain.(Ahmad)