logo

HAUSA

An yaba da matakan da gwamnatin kasar Sin take dauka domin karfafa hadin-gwiwa da sauran kasashe wajen samar da allurar riga-kafin annobar COVID-19

2021-01-20 20:43:58 CRI

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying, ta bayyana a yau Laraba cewa, kawo yanzu, akwai kasashe sama da 40, wadanda suka bayyana bukatar shigar da allurar riga-kafin annobar COVID-19 da kasar Sin ta samar kasashen su. Bisa habakar kamfanoni daban-daban, kasar Sin za ta kara samar da alluran ga kasashe mabukata.

Madam Hua ta ce, kamfanonin kasar Sin na gudanar da hadin-gwiwa da kawayensu na kasashe sama da 10, a fannin nazari, gami da samar da allurar riga-kafin cutar COVID-19.

Game da kasashen dake da matukar bukatar allurar, da wadanda suka amince da allurar kirar kasar Sin, gami da kasashen da suka riga suka bada izinin amfani da allurar kirar kasar Sin cikin gaggawa, kamfanonin Sin sun riga sun fara fitar da alluran, ko gudanar da shawarwari tare da su, kuma akasarinsu kasashe ne masu tasowa.

Kawo yanzu, kasashen da suka riga suka aminta da amfani da allurar kirar kasar Sin sun hada da hadaddiyar daular Larabawa, da Bahrain, da Masar, da Jordan, da Turkiyya, da Indonesiya, da kuma Brazil.(Murtala Zhang)