logo

HAUSA

Gwamnatin Kamaru ta lashi takobin mayar da martani kan kisan da aka yi wa dakarunta

2021-01-20 09:44:37 CRI

Ministan kula da yankunan Kamaru, Paul Atanga Nji, ya ce gwamnati za ta dauki matakai masu tsauri, kan ‘yan awaren da suka kashe jami’an tsaron kasar a yankin arewa maso yammacin kasar dake da rinjayen masu amfani da harshen Ingilishi, wanda kuma ke fama da rikici.

Wasu rahotannin tsaro, sun bayyana cewa, akalla jami’an tsaron Kamaru 12 aka kashe a hare-haren ‘yan aware tun daga farkon watan nan.

A cewar wasu majiyoyi daga bangaren tsaro, ‘yan aware sun sabunta inganta kai hare-hare yankin, bayan kura ta dan lafa a watan Disamba.

An shafe sama da shekaru 3 ana gwabza fada tsakanin ‘yan aware masu dauke da makamai da dakarun gwamnati, a yankunan Kamaru 2 na arewa maso yammaci da kudu maso yammaci dake da rinjayen masu amfani da harshen Ingilishi, inda ‘yan aware ke yunkurin kafa ‘yantacciyar kasa da suke kira da Ambazonia. (Fa’iza Mustapha)