logo

HAUSA

Babban sakataren WHO ya bukaci a yi wa mutane allurar rigakafi cikin adalci

2021-01-19 10:53:43 CRI

Jiya Litnin, aka kira taron kwamitin zartaswa na hukumar lafiyar duniya ta WHO karo na 148. A jawabinsa na bude taron, babban sakataren hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi kira ga kasashen duniya da su yi wa al’ummomi allurar rigakafi cikin adalci.

An kira taron da zai gudana daga ranar 18 zuwa 26 ga wata ta kafar bidiyo, inda za a tattauna jadawalin babban taron kiwon lafiyar duniya da gabatar da kudurin gudanar da babban taron kiwon lafiyar duniya.

Tedros ya ce, an samar da allurar rigakafi mai inganci bayan shekara daya da barkewar cutar COVID-19. Wannan wata babbar nasara ce da aka cimma a fannin kimiyya. Amma kuma, hadarin dake gabanmu a halin yanzu, shi ne rashin adalci wajen raba allurar.

Ya jaddada cewa, bai dace a yiwa matasa masu lafiya a kasashe masu ci gaba allurar rigakafin cutar COVID-19 kafin masu aikin kiwon lafiya da tsoffafi dake kasashe masu fama da talauci ba. A nan gaba, za a samu isassun allurar rigakafin cutar COVID-19, amma a halin yanzu, ya kamata mu hada, mu kuma ba da fifiko ga mutanen da suka fi fuskantar hadarin kamuwa da cutar COVID-19 cikin kasa da kasa. (Maryam)