logo

HAUSA

Jawaban shugaba Xi Jinping ya ba da jagoranci ga hadin kan bil Adama

2021-01-18 14:21:10 CRI

Jawaban shugaba Xi Jinping ya ba da jagoranci ga hadin kan bil Adama_fororder_italiya

Wasu shekaru 4 da suka wuce, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin kaddamar da taron dandalin tattalin arzikin duniya na shekarar 2017, tare da gabatar da jawabi kan dabarar raya tattalin arzikin duniya. Daga baya a hedkwatar MDD dake Geneva na kasar Switzerland, shugaban ya sake yin jawabi don bayyana burinsa na kafa wata al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya.

Dangane da wadannan jawabai masu muhimmanci, jakadan kasar Sin dake kasar Switzerland Wang Shiting, da wani shahararren masanin kasar Italiya mai nazarin batutuwan da suka shafi kasar Sin, Francesco Maringio, sun ce har zuwa yanzu kalmomin shugaban kasar Sin na ci gaba da ba da jagoranci ga aikin hadin kan bil Adama.

Wang Shiting, shi ne jakadan kasar Sin a kasar Switzerland, a cewarsa, barkewar annobar COVID-19 ta haifar da illoli ga tsare-tsaren duniya, musamman ma a fannin tattalin arziki da ciniki. Wang ya ce, annobar ta sa kasashe daban daban kara nuna ra’ayin son kai, inda wasunsu ke neman fakewa da batun kare hakkin dan Adam wajen sanya wa sauran kasashen takunkumi, ko kuma daukar matakai na kashin kai da fin karfi yayin da suke hulda da sauran kasashe.

A ganin jami’in na kasar Sin, matakan ba za su haifar da da mai ido ba. Idan an tuna da jawabin da shugaba Xi Jinping ya yi wasu shekaru 4 da suka wuce, a lokacin ya riga ya bayyana sarai cewa, tsarin tattalin arzikin duniya ya riga ya zama mai dunkulewa sosai, ba zai yiwu a sake kasa shi kashi daban daban ba. Sa’an nan game da matakan da za a iya dauka don farfado da tattalin arzikin kasa da kasa, jakada Wang ya ce,

“Tuni shugaba Xi ya riga ya bayyana mana matakan, wato a yi kokarin amfani da damammakin da za a iya samu, don yin hadin gwiwa, da daidaita tsarin dunkulewar tattalin arzikin duniya, ta yadda za a iya samun karuwar tattalin arziki mai dorewa, da tsarin hadin kai da zai iya amfanawa kowa, da wani tsarin kula da al’amuran duniya bisa adalci.”

A cewar jami’in, daukacin bil Adama wata al’umma ce mai makomar bai daya, don haka ba za mu samu daidaita matsalolin da ake fuskantar ba, sai ta hanyar hadin gwiwar da kokari tare.

Da ma a cikin jawabin da shugaba Xi Jinping ya gabatar, mai taken “Kafa wata al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya”, ya ce, wani babban burin da daukacin bil Adama suka sanya, shi ne neman samun zaman lafiya, da ci gaban kasa. Yayin da duniyarmu ke fuskantar kabubale daban daban, shawarar da kasar Sin ta gabatar ita ce, kafa al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya a duniya, don tabbatar da samar da alfanu ga kowa, da raba moriya tare.

A ganin Francesco Maringio, wani masani na kasar Italiya, mai nazarin batutuwan da suka shafi kasar Sin, wani babban dalilin da ya sa ake ta samun matsaloli a duniya, shi ne rashin daidaito a tsakanin kasashe da al’ummu daban daban. Kana shawarar da kasar Sin ta gabatar ta kafa al’umma mai makomar bai daya, za ta iya zama wata hanya mai dacewa da za a iya binta don daidaita matsalolin da ake fuskanta a duniya. Ya ce,

“Jawabin da shugaba Xi Jinping ya yi, ya nuna mana wata sabuwar hanyar kula da harkokin siyasa na kasa da kasa. Ya kamata mu yi kokarin daidaita matsalar rashin daidaito a cikin wata kasa ko kuma wani yanki, inda kamar yadda muka saba gani a wasu kasashen yammacin duniya, masu kudi na kara samun kudi, yayin da talakawa ke fama da rashin damar samun wadata. Sa’an nan a yi kokarin magance rashin daidaito tsakanin kasashe.”

A cewar masanin na kasar Italiya, yadda kasar Sin ta samu damar kawar da talauci baki daya a cikin gida a karshen shekarar 2020, wani babban ci gaba ne a kokarin kawar da matsalar rashin daidaito tsakanin al’ummomi.

A yayin da ake tinkarar cutar COVID-19, babu wata kasa da za ta iya daidaita wannan batu ita kadai, ba tare da hadin gwiwa da sauran kasashe ba. Cikin jawabin da shugaba Xi Jinping ya yi wasu shekaru da suka wuce, ya riga ya shawarci hukumar lafiya ta duniya WHO ta kara taka mihimmiyar rawa a kokarin jagorantar ayyukan binciken annoba, da raba fasahohi tsakanin kasashe daban daban. Dangane da maganar shugaban, mista Maringio ya ce,

“Maganarsa ta burge ni sosai. Yayin da ake samun barkewar cutar COVID-19 a kasashen yammacin duniya, kasar Sin ta riga ta shawo kan yaduwarta. Kana ta samar da taimako ga kasashe daban daban, ciki har da Italiya. Ta haka za mu iya ganin yadda kasar Sin take kokarin cika alkawarinta.”(Bello Wang)

Bello