logo

HAUSA

Ziyarar Wang Yi a kasar Indonesiya za ta inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu bayan annoba

2021-01-14 20:54:37 CRI

Yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya yi bayani kan sakamakon da aka cimma yayin ziyarar ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a kasar Indonesiya. Yana mai cewa, kasar Sin da kasar Indonesiya sun cimma matsayi daya kan fannoni guda biyar, da suka hada da yin hadin gwiwa wajen yaki da annoba, zurfafa hadin gwiwarsu a fannoni daban daban, inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen dake yankin gabashin Asiya, da kiyaye zaman lafiya a tekun kudancin Sin, da kare da inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa.

A safiyar yau, kafofin watsa labarai na kasar Indonesiya sun watsa rahotanni game da yi wa shugaban kasar allurar rigakafin cutar COVID-19 da kasar Sin ta samar kai tsaye, a cewarsu, shugaban kasar Joko Widodo shi ne mutum na farko da aka yi masa allurar rigakafi a duk fadin kasar.

A yayin ganawarsa da minista Wang Yi, shugaba Joko Widodo ya nuna godiya ga kasar Sin, saboda samar wa kasarsa da allurar rigakafin, ya kara da cewa, an cimma sakamako da dama a fannin kiwon lafiya bisa hadin gwiwar kasar Sin da kasar Indonesiya. (Maryam)