logo

HAUSA

Cinikayya ta yanar gizo ta kara yawan kudin shigar manoman kasar Sin, in ji ma’aikatar noma da raya karkara

2021-01-14 10:52:35 CRI

Rahotanni daga ma’aikatar noma da raya karkara ta kasar Sin, sun bayyana cewa, cinikayya ta yanar gizo, ta habaka yawan kudin shiga da manoman kasar ke samu, tare da ba da gudummawa, ga kokarin kasar na raya kauyuka.

Zeng Yande, ma’aikaci ne a hukumar, ya kuma shaida da cewa, a shekarar 2019, darajar hada hadar cinikayya ta yanar gizo a fannin, ta kusa kaiwa kudin Sin yuan biliyan 400, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 61.9. Zeng wanda ya bayyana hakan jiya Laraba, yayin wani taron manema labarai, ya ce yanayin yankunan karkara ya samu gagarumin ci gaba, musamman a fannonin bunkasa cinikayya ta yanar gizo, ciki har da ingantuwar fannin sadarwa da na hidimar aikewa da sakwanni, inda a ‘yan shekarun baya bayan nan, fasahar wayar salula ta 4G, ta karade kaso 98 bisa dari na kauyukan kasar.

Kaza lika jami’in ya ce, cikin shekaru kusan 3 da suka gabata, Sin ta aiwatar da manufofinta na raya karkara. Wanda hakan ya sanya manoma samun gagarumin sauyi ta fuskar kudaden shiga, tare da rage gibin kudin shiga tsakanin su da mazauna birane. (Saminu)