logo

HAUSA

Wang Yi: Sin na goyon bayan cikakken tsarin cudanyar dukkanin sassa

2021-01-14 10:46:23 CRI

Mamban majalissar gudanarwar kasar Sin kuma ministan wajen kasar Wang Yi, wanda ke ziyarar aiki a kasar Indonesia, ya bayyana aniyar kasar Sin ta ci gaba da goyon bayan cudanyar dukkanin sassan kasa da kasa, yana mai cewa kamata ya yi a martaba dokokin da suke da alaka da wannan manufa, tare da kaucewa raba kafa wajen aiwatar da manufofin.

Wang ya kara da cewa, tsarin cudanyar dukkanin sassa na ainihi, na nufin riko da dokokin MDD, da martaba ka’idojin huldar kasa da kasa, da martaba ikon mulkin dukkanin kasashen duniya manya da kananan, da ma daidaito a tsakaninsu.

Wang Yi ya ce, amincewa da cudanyar dukkanin sassa na nufin rungumar dukkanin bambance bambance dake tsakanin sassa daban daban, da martaba ikon ci gaba, da salon bunkasuwar kasashe mabanbanta, tare da yayata dimokaradiyya yayin da ake gudanar da cudanya tsakanin sassan kasa da kasa.

Ministan wajen na Sin, ya tabbatar da cewa, Sin na adawa da kafa wani rukuni na siyasa da sunan cudanyar kasashe, tana kuma kin manufar kakabawa dukkanin kasashen duniya wasu ka’idoji da tsirarrun kasashe suka kafa. A hannu guda kuma, Sin ba za ta amince da gindaya wasu sharuddan kashin kai, a matsayin hanyar kafa rukunin goyon bayan wani sashe, don muzgunawa wasu kasashen ba.   (Saminu)