An yi gwajin jirgin UAV kirar kasar Sin
2021-01-14 10:32:38 CRI
Kamfanin raya ayyukan kimiyya da fasahar samaniya na kasar Sin, ya ce ya cimma nasarar gudanar da gwajin farko na wani nau’in jirgin sama samfurin WJ-700 maras matuki, jirgin da kamfanin ya ce yana iya tashi kololuwar sama, ga sauri da kuma juriya. Baya ga hakan, ana iya amfani da jirgin wajen kaddamar da hari, yana kuma iya yin ayyukan suntiri da sanya ido.
A cewar kamfanin da ya kirkiri jirgin, WJ-700 yana iya dakon wasu kayayyaki, kana juriyar aikin sa ta kai wani babban matsayi. Kamfanin ya ce yana fatan fara cinikayyar jirgin a kasuwannin cikin kasar Sin da kuma na ketare, nan da shekaru 5 zuwa 10 masu zuwa. (Saminu)