logo

HAUSA

Dabarar da Xi ya gabatar game da fuskantar kalubalen duniya

2021-01-14 20:51:21 CRI

A watan Janairu na shekarar 2017, Xi Jinping ya taba yin cikakken bayani game da ra’ayin samar da makomar bai daya ga dukkanin bil Adama yayin wani taron MDD da aka gudanar a birnin Geneva, wannan ita ce dabarar da Xi ya gabatar game da yadda za a fuskanci babbar kalubalen duniya. Yanzu, shekara daya ke nan, da aka yi fama da yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, ra’ayin da Xi ya gabatar ya ba da amsa ga kasa da kasa, game da yadda za a fuskanci wannan matsala.

A shekarar da ta gabata, shugaba Xi ya yi ganawa da yin shawarwari har sau 87 ta yanar gizo tare da shugabannin kasashen duniya da na hukumomin kasa da kasa, da halartar taruka na musamman game da yaki da annoba a tsakanin bangarori daban daban guda 22, kamar babban taron hukumar kiwon lafiyar duniya da taron kolin shugabannin kungiyar G20 game da yaki da cutar COVID-19 da sauransu, lamarin da ya ba da jagoranci ga kasa da kasa ta fuskar aikin yaki da annobar cutar COVID-19.

Ban da haka kuma, kasar Sin ta gudanar da aikin ba da taimakon jin kai ga kasashe da dama a shekarar 2020, inda ta samar da abin rufe hanci da baki sama da biliyan dari 2, da riguna kariya sama da biliyan 2, da kuma na’urorin gwajin kwayoyin cutar COVID-19 miliyan dari 8 ga kasashe da dama. Ta kuma ba da taimakon yaki da cutar ga kasashe sama da 150 da kungiyoyin duniya guda 10, baya ga aika tawagogin ma’aikatan lafiya 36 zuwa kasashe 34 dake da bukata.

Haka kuma, a matsayinta na kasar dake kan gaba a aikin nazarin allurar rigakafin cutar COVID-19, kasar Sin ta kafa cibiyar nazarin allurar rigakafin COVID-10 ta kasashen BRICS. A halin yanzu, ban da kasashen Brazil, Indonesiya, Masar da Turkiya da sauransu, akwai Karin kasashe masu tasowa da suka samu allurar rigakafi daga kasar Sin.

Ra’ayin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga dukkanin bil Adama na ci gaba da samun amincewa tsakanin kasashen duniya, har ma an shigar da ra’ayin cikin muhimmiyar takardar MDD.

Shin Yaya za a fuskanci kalubalolin dake gabanmu bayan wannan annoba? Amsar ita ce, yin kokarin raya makomar bai daya ga daukacin bil-Adama. (Maryam)