logo

HAUSA

Matsayin Cinikayyar kayayyakin Sin a ketare ya kai koli a 2020 da kalubalen da aka fuskanta

2021-01-14 13:50:24 CRI

Kididdiga ta nuna cewa, jimilar kayayyakin shige da fice na kasar Sin a shekarar 2020, ya karu da kaso 1.9 zuwa yuan triliyan 32.16, kwatankwacin dala triliyan 5, adadin da ya kai matsayin koli duk da matsalar jigilar kayayyaki da aka samu a duniya.

A cewar kakakin hukumar kwastan ta kasar Sin, Li Kuiwen, duk da kalubalen tattalin arziki da cinikayya da aka fuskanta a 2020, kasar Sin ta zama kasa daya tak a duniya da ta samu ci gaba ta fuskar cinikayyar kayayyaki a ketare. (Fa’iza Mustapha)