logo

HAUSA

Majalisar wakilan Amurka ta tsige Trump inda ya zama shugaban Amurka na farko da aka tsige har sau biyu

2021-01-14 09:40:37 CRI

A ranar Laraba majalisar wakilan Amurka ta jefa kuri’ar tsige shugaban kasar Donald Trump, bisa tuhumarsa da laifin tunzura mabiyansa wajen tada bore a zauren majalisar a makon jiya, shugaban ya shiga cikin tarihin zama shugaban Amurka na farko da aka tsige har sau biyu daga mukamin shugabancin kasar.

Ko a watan Disamban shekarar 2019 ma, sai da majalisar dokokin Amurkar ta tsige shugaba Trump, sakamakon tuhumarsa da laifukan saba dokar kasa, da yiwa majalisar dokokin kasar zagon kasa game da batun mu’amalarsa da kasar Ukraine. Sai dai majalisar dattijan kasar ta wanke shi daga zargin, sakamakon gaza samun rinjaye na kashi biyu bisa uku na yawan sanatocin da suka goyi bayan kudurin tsige shugaban.(Ahmad)