logo

HAUSA

Turkiyya ta karbi riga kafin COVID-19 na kasar Sin

2021-01-14 12:44:48 CRI

Ministan lafiya na kasar Turkiyya, Fahrettin Koca, ya karbi riga kafin COVID-19 da kamfanin Sinovac na kasar Sin ya hada, yayin wani shirin kai tsaye ta kafar talabijin da aka watsa ga al’ummar kasar a jiya. A kuma lokacin, an yi wa mambobin kwamitin kwararru mai tinkarar cutar a kasar, allurar riga kafin na Sin.

Fahrettin Koca, ya bayyana yayin taron manema labaran cewa, riga kafin na Sin na da aminci kuma za a fara yi wa ma’aikatan lafiya na kasar allurar daga yau 14 ga wata. Ya ce yi wa ‘yan siyasar kasar alluran, zai zama misali ga al’umma, domin dole sai an yi musu kafin harkokin rayuwa su daidaita kamar yadda suke. (Fa’iza Mustapha)