logo

HAUSA

Kasar Sin ta bukaci Amurka da ta daina tsoma baki a harkokin yankin Taiwan

2021-01-14 20:44:53 CRI

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bukaci Amurka da ta martaba manufar kasar Sin daya tak a duniya, da tanade-tanaden dake kunshe cikin sanarwoyin hadin gwiwa guda uku da kasashen biyu suka sanyawa hannu, ta kuma gaggauta daina sanya batun na siyasa kan harkokin da suka shafi yankin Taiwan na kasar Sin.

Zhao Lijian ya bayyana haka ne Alhamis din nan, a taron manema labaran da aka saba shiryawa, lokacin da yake mayar da martani kan kalaman da mataimakin sakataren wajen Amurka Keith Krach ya wallafa a kafar sada zumunta cewa, sakataren wajen Amurka Mike Pompeo ya baiwa yankin na Taiwan matsayin kasa mai ‘yanci.

Da yake amsa tambaya game da tattaunawar da jakadiyar Amurka a MDD Kelly Craft ta yi da jagorar yankin Taiwan Tsai Ing-wen ta kafar bidiyo a yau kuwa, jami’in na kasar Sin ya ce, kasarsa tana adawa da duk wata hulda tsakanin jami’an Amurka da na yankin Taiwan. Yana mai cewa, wasu ‘yan siyasar Amurka za su yabawa aya zaki, kan munanan abubuwan da suka aikata kan yankin Taiwan.(Ibrahim)