logo

HAUSA

Jami’an bankin Duniya: Farfadowar tattalin arzikin kasar Sin zai amfani duniya

2021-01-13 19:26:20 CRI

Jami’an bankin duniya da dama sun bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai yi gagarumin farfadowa a shekarar 2021 da muke ciki, zai kuma ba da babbar gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.

Jami’an sun bayyana haka ne, yayin wani taron karawa juna sani da bankin ya shirya Larabar. Wani sabon rahoton da bankin ya fitar mai taken “hasashen yanayin tattalin arziikin duniya” ya nuna cewa, sakamakon koma bayan tattalin arziki dan kadan da aka fuskanta a wasu manyan kasashe masu karfin tattalin arziki, da kuma yadda tattalin arzikin kasar Sin ya kara farfadowa fiye da yadda aka yi zato, karayar da tattalin arzikin duniya ya shiga a shekarar 2020 ba za ta kai yadda aka yi hasashe a baya ba. Daga cikin wadannan kasashe, ana hasashen tattalin arzikin kasar Sin zai bunkasa da kaso 2 cikin 100. (Ibrahim)