logo

HAUSA

Wata ‘yar Italiya ta kamu da cutar COVID-19 a watan Nuwanba na shekarar 2019

2021-01-13 09:57:58 CRI

Wata ‘yar Italiya ta kamu da cutar COVID-19 a watan Nuwanba na shekarar 2019_fororder_0113-1

Bisa labarin da aka bayar a tashar internet ta jaridar La Repubblica ta kasar Italiya a ranar 11 ga wata, an ce, tawagar nazari ta kasa da kasa, wadda jami’ar Milan ta jagoranta, ta gano kwayar dabi’ar halitta ta cutar COVID-19 a jikin samfurin da aka dauka daga wata mace mai shekaru 25 da haihuwa, bayan ta kamu da gyambon fata, aka kuma gabatar da nazarin ta a ranar 10 ga watan Nuwanba na shekarar ta 2019.

Ban da wannan kuma, an gano kwayoyin garkuwar jiki ta cutar COVID-19, a yayin wani binciken jini da aka yi mata a watan Yuni na shekarar 2020. A ganin masu nazari na jami’ar ta Milan, wannan ne karon farko da aka gano dan Adam dauke da cutar COVID-19 ya zuwa yanzu. (Zainab)