logo

HAUSA

Ya kamata kasar Amurka ta dauki alhakin aikace-aikacen kabilanci

2021-01-13 20:58:59 CRI

Ya kamata kasar Amurka ta dauki alhakin aikace-aikacen kabilanci_fororder_sha

Wasu ‘yan siyasan kasar Amurka sun saba da shafa wa kasar Sin kashin kaza. Kana sun ci gaba da yin haka a lokacin da wa’adin gwamnatin kasar mai ci ke shirin karewa, inda suke zargin kasar Sin da “neman kawar da dukkan ‘yan kabilar Uygur”.

Wai dokin mai baki aka ce ya ji gudu. Shaidu da muhimman bayanan alkaluma sun nuna cewa, kidayar al’umma da aka yi a kasar Sin ta nuna cewa, tsakanin shekarun 2010 zuwa 2018, yawan ‘yan kabilar Uygur dake zama a kasar ya karu daga miliyan 10.17 zuwa miliyan 12.72, inda karuwar ta kai kashi 25.04%.

Hakika a duk lokacin da aka ambaci batun kisan kiyashi da neman kawar da wata al’umma, lamarin dake faruwa ke nan a kasar Amurka, wadda ta dade tana nuna ra’ayi na kabilanci.

Tarihin kasar Amurka ya nuna yadda gwamnatin kasar ta yi kokarin cin zarafi da kashe ‘yan asalin kasar da ake kira Red Indian. Lamarin da ya sanya yawan al’ummar ta ragu daga miliyan 5 na shekarar 1492, zuwa dubu 250 a farkon karni na 20.

Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da samun aikace-aikacen kabilanci sosai a kasar Amurka, inda yawan ‘yan kasar bakar fata da suka kamu da cutar COVID-19 ko suka mutu sakamakon cutar, ya ninka na farar fata har sau 5.

Ban da wannan kuma, wani binciken ra’ayin jama’a da aka yi a kasar Amurka a shekarar 2017 ya nuna cewa, kashi 75% na Musulman kasar sun ce ana nuna musu bambanci. Kana cikin wasu aikace-aikacen kin jinin Musulmai da aka yi a kasar Amurka a shekarar 2017, fiye da sulusinsu, an yi su ne sakamakon yadda hukumomin kasar suka rura wutar rikici.

Kana a nasa bangare, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo mutum ne dake matukar kin jinin Musulmai. Yana goyon bayan takaita shigowar Musulmai cikin Amurka. Duk da haka, ya nuna cewa yana mai da hankali matuka kan muradun ‘yan kabilar Uygur ta kasar Sin, wadanda su ma Musulmai ne. Wannan wani abun mamaki ne.

Don haka, za mu iya fahimtar cewa, yadda kasar Amurka ke shafawa kasar Sin bakin fenti, tamkar barawo ne ya ke ihun a kama barawo! Ya kamata Amurka ta dauki alhakin munanan ayyukan da take aikatawa. Gwano aka ce ba ya jin warin jikinsa. (Bello Wang)

Bello