logo

HAUSA

Sin na kokarin ba da gudunmawarta ga aikin kiwon lafiya a duniya

2021-01-13 13:52:11 CRI

Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, ya fitar da wata takardar bayani, kan hadin kan kasa da kasa da Sin za ta yi a sabon karni, inda aka nuna cewa, cutar COVID-19 ta kawo babbar barazana ga zaman rayuwa da lafiyar jama’ar kasashen daban-daban, ta kuma lahanta fannin kiwon lafiya na kasa da kasa.

Don haka bisa bukatun wasu kasashe, Sin tana ba da gudunmawarta gwargwadon karfinta ga aikin kiwon lafiya a duniya.

Allurar rigakafi ta zama mataki mai muhimmanci da aka sa ran yakar cutar COVID-19. Sin tana nacewa ga hadin kai da kasashen duniya kan samar da allurar, yanzu ana aikin gwaji kan allurar samfura iri daban-daban na mataki 3 da Sin ta samar a Argentina da Peru da Brazil, Indonesiya da sauransu, haddadiyar daular Larabawa UAE da Bahrain sun amince da amfani da allurar da kamfanin Sinopharm na kasar Sin ya samar. Ban da wannan kuma, kasar Masar ta sanar da amfani da irin wannan allurar cikin gaggawa, minista mai kula da kiwon lafiya da jama’a Hala Zayed ta ce:

“Masar da Sin suna taimakawa juna wajen yakar wannan mummunar cutar, ina godiya sosai ga taimakon da Sin take baiwa kasar. Ana gudanar da aikin gwaji mataki na 3 lami lafiya, abin da ya shaida cewa allurar da Sin ta samar na da aminci. Masar na fatan kara hadin kai da kasar Sin a wannan fanni.”

Ban da wannan kuma, Sin ta tura tawagogin masana jiyya da kayayyakin tallafawa ga kasashe da suka matukar bukata don rarraba fasaha da dabarun yakar cutar. Ya zuwa tsakiyar watan Disamba na bara, Sin ta ba da tallafi ga kasashe 150 da kungiyoyin kasa da kasa 9, da kuma tura tawagogin masana 36 zuwa kasashe 34. Dadin dadawa, ta samarwa sauran kasashe marufin baki da hanci sama da biliyan 200, tufafin rigakafi biliyan 2, da kayayyakin gwajin cutar miliyan 800. Mataimakiyar shugaban cibiyar nazarin batutuwan kasa da kasa Su Xiaohui ta ce:

“Wannan cutar abokiyar gaba ce ga duk Bil Adama, kowa na shiga wannan yaki. Kasashe da dama sun fahimci cewa, akwai bukatar jama’ar duniya su hada kansu don yakar cutar. Har ma sun fahimci ma’anar ra’ayin raya kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya.”

Bisa wannan takardar da aka bayar, Sin za ta ci gaba da ba da gudunmawarta wajen goyon bayan WHO da dai sauran kungiyoyin kiwon lafiya, tare kuma da yin kira ga kasashen duniya da su kara goyon bayan WHO a siyasance da zuba karin kudade, ta yadda za a yi amfani da albarkatun duniya wajen yakar cutar. Ban da wannan kuma, ci gaba da goyon bayan G20 da APEC da BRICS da SCO da dai sauran kungiyoyin kasa da kasa da su yaki cutar cikin hadin kai. Su Xiaohui ta ce, ana fahimtar wajibcin raya kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya a fannin kiwon lafiya:

“Ana bukatar tuntubar juna da yin musanyar kayayyakin yaki da cutar a yayin da kasashen duniya ke kokarin yakar cutar. Saboda haka, ana fatan baiwa WHO da dai sauran kungiyoyin kasa da kasa goyon-baya.”

Malam Bahaushe kan ce, guntun gatarinka ya fi sari ka ba ni. Har kullum kasar Sin ta kan rarraba fasahohi gami da dabarunta domin gina kasashe masu tasowa. Bayanin ya ce, Sin za ta ci gaba da taimakawa kasashe masu tasowa wajen kafa cikakken tsarin kiwon lafiya, da hada kai da WHO don taimakawa kasashe masu tasowa musamman ma kasashen Afrika wajen inganta tsarinsu na kiwo lafiya, ta hanyar kafa asibitoci hadin kai 30 a Afrika da gaggauta kafa cibiyar magance cututtuka masu yaduwa a Afrika da dai sauransu. Matakan da za su taimakawa wadannan kasashe wajen karfafa kafinsu na tinkarar batun kiwon lafiya na ko ta kwana. (Amina Xu)