logo

HAUSA

Sin ta bukaci a karfafa hadin gwiwa wajen yaki da ta’addanci

2021-01-13 13:56:15 CRI

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya bukaci a karfafa hadin gwiwa a fagen yaki da ta’addanci.

Yayin wata muhawara kan barazanar da ayyukan ta’addanci ke haifarwa ga zaman lafiya da tsaro a duniya, Zhang Jun, ya ce ya zama wajibi a zurfafa cimma matsaya guda da karfafa hadin gwiwa wajen yaki da ta’addanci.

Ya ce ta’addanci makiyi ne ga dukkan bil Adama, kuma yaki da shi, hakkin ne na bai daya da ya rataya a wuyan al’ummun duniya, yana mai cewa, hadin gwiwa ne makami cin galaba kansa.

Da yake jawabi kan yadda za a yaki ta’addanci, wakilin na Sin, ya ce dole ne a rungumi matakin hadin gwiwa da bijirewa zabe yayin da ake yaki da ta’addanci.

Ya ce babu ta’addanci mai kyau ko mara kyau. Dole ne a yi tir da dukkanin ayyukan ta’addanci ba tare da la’akari da wuri ko lokaci ko wanda ya aikata ba. Ya kara da cewa, dole ne a kauracewa nuna fuska biyu ko zabar abun da za a kira da ta’addanci.

Har ila yau, ya ce ya kamata kokarin kare aukuwar ayyukan ta’addanci ya kasance bisa shawo kan tushen matsalar.

Bugu da kari, ya ce wajibi ne a dauki ingantacciyar dabarar da ta kunshi tsarin siyasa da tattalin arziki da shari’a da zamantakewa domin kawo karshen ci gaban ayyukan ta’addanci da tsattsauran ra’ayi. (Fa’iza Mustapha)