logo

HAUSA

Pence ya shaidawa Pelosi rashin amincewarsa da aiwatar da kuduri na 25 kan shugaba Trump

2021-01-13 14:27:46 CRI

Mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence, ya shaidawa kakakin majalissar dokokin Amurka Nancy Pelosi cewa, bai zai amince da aiwatar da kudurin nan na 25, da ya tanaji damar tsige shugaban kasar Donald Trump ba. Mr. Pence ya bayyana hakan ne a jiya Talata, jim kadan gabanin majalissar ta fara kada kuri’un neman amincewa da bukatar.

Hakan dai na zuwa ne, bayan da ’yan majalissar tsagin jam’iyyar dimokarat ke shirin kada kuri’un neman amincewa da kudurin neman yardar Mr. Pence na a tsige shugaba Trump, bisa zarginsa da tunzura boren da ya auku makon da ya gabata a “Capitol Hill”.

Amincewar mataimakin shugaban kasar ne matakin farko, kafin ’yan majalissar su fara aiwatar da matakai na gaba na tumbuke shugaba Trump, kamar dai yadda ’yan majalissar mai rinjayen jam’iyyar dimokarat suka bayyana.

To sai dai kuma, duk da rashin amincewar da Pence ya nunawa wannan bukata, wadda ke cikin kundin tsarin mulkin kasar, ’yan majalissar wakilan sun sha alwashin kada kuri’un neman tsige Trump a ranar Laraba.

Kafin hakan a jiya Talata, lokacin da yake duba katangar kan iyaka da ake ginawa a Alamo na jihar Texas, shugaba Trump ya bayyana yunkurin tsige shi a matsayin abun dariya, yana mai cewa ba ya fuskantar wata barazana daga tanajin kudurin mai lamba 25.  (Saminu)